Samiha Ayoub

Samiha Ayoub ( Larabci: سميحة أيوب‎ ) 'yar wasan kwaikwayo ce ta ƙasar Masar wacce tayi fice a wasanninta na fage, a cikin fina-finai da kuma shirye shiryen talabijin. A cikin shekarar 2015, ta sami lambar yabo ta (Nile Award in the Arts),[1][2] kuma a cikin wannan shekarar dai, (the large hall in the National Theater) ya saka sunan ta don girmama irin rawar da kuma jarumar take takawa a sana'arta ta fitowa a cikin shirye-shiryen wasanni sinima da wasan kwaikwayo, da gudummawar da kuma take bayarwa a (theatrical arts) a lokacin wasan kwaikwayo a Masar.[3]

Samiha Ayoub
Rayuwa
HaihuwaKairo, 8 ga Maris, 1932 (92 shekaru)
ƙasaMisra
Ƴan uwa
Abokiyar zamaAhmed El-Nahass (en) Fassara
Mahmoud Moursy (en) Fassara
Karatu
HarsunaLarabci
Sana'a
Sana'aJarumi
IMDbnm0044066
Samiha Ayoub

Tarihin Rayuwa

An haifi Samiha Ayoub a Shubra, Alkahira a shekara ta 1932.

Ta yi karatu a Makarantar Nun, sannan ta shiga Acting institute a shekarar 1952. Ci gabanta ya zo ne bayan rawar da ta taka a cikin fim ɗin "Samara" da kuma Rabaa ElAdawya wanda shirye-shirye ne masu dogon Zango na ƙafar sadarwa ta rediyo (radio series).

Ayyuka

Daga shekarar 1972 – 1975, Ayoub ta mallaki gidan wasan kwaikwayo na zamani, kuma daga 1975 – 1985, ta kasance shugabar gidan wasan kwaikwayo ta Al-Qawmy.

Ta yi wasan kwaikwayo a cikin shahararrun miniseries na talabijin El Miraya tare da Salah Zulfikar a shekarar 1984.[1][4]

Wasanni

  • Al-Bakhil (Bakhil)
  • Kobry Al-Namoos (Gadar Sauro) [1]
  • Sikkat Al-Salama (Hanyar Madaidaiciya) [1]

Fina-finai

  • Motashareda
  • Shatea Al-Gharam Wal Wahsh
  • Bein El Atlal (1959) [1]
  • Tita Rahiba (2012) [1]
  • El-Leila El-Kebira (2015) [1]

Talabijin

  • El Miraya (1984)

Iyali

Ta yi aure sau uku, ta auri jarumi Mohsen Sarhan, bayan nan ta auri jarumi Mahmoud Morsy, da kuma marubucin wasan kwaikwayo Sa'ed Eddine Wihbe (Saad Eddin Wehbe).[5]

Manazarta