Rikicin Zariya na 2015

Rikicin Zariya na cikin shekarar 2015 rikici ne da ya faru tsakanin Sosojin Najeriya da yan kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (yan Shi'a mabiya Ibrahim Zakzaky) a birnin Zariya na Jihar Kaduna a Tataraiyar Najeriya. Anyi rikicin ne ranar 12 ga Disambar shekarar 2015.[1][2][3][4] Akalla fararen hula 348 ne suka rasa rayukan su, sannan kuma an binne wasu gawawaki 347 a rami ɗaya kuma a sirrance.[5]

Infotaula d'esdevenimentRikicin Zariya na 2015
Map
 11°04′N 7°42′E / 11.07°N 7.7°E / 11.07; 7.7
IriKisan Kiyashi
WuriZariya

Yanar gizoislamicmovement.org
Zaria a yau

Rundunar sojin Najeriya ta ce tabude wuta ne domin mayar da martani sakamakon ƙoƙarin da almajiran na Zakzaky sukayi na farmakar shugaban rundunar sosojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai. Sai dai su yan shi'ar da wasu ƙungiyoyin kare Haƙƙin dan'adam sun musanta wannan bayanin na sosjoji, inda sukace rundunar sojin Najeriya ta afka masu ne batare da hakkin suba.[1][6][7][8].

Faruwar rikicin

Ranar 12 ga Disamba shekarar 2015 ne a Zariya sojojin Najeriya suka koka kan cewar Yan Shi'a sun farmake su. Rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 348 yayin da wasu da dama kuma suka sami raunuka.[4] Shima jagoran na ƙungiyar ta Harkar Musulunci a Najeriya Ibrahim Zakzaky ya samu raunuka sakamakon harbi da harsahi da akayi masa tare kama maidakinsa Zeenah Ibrahim da wasu daruruwan mabiyansa.[9]

An kone wasu da rayukan su, inji ƙungiyar kare Haƙƙin dan'adam ta ƙasa da ƙasa wato Amnesty International.[10]

Itama ƙungiyar kare Haƙƙin dan'adam ta Human Right Wach ta ce Gwamnatin Najeriya ta binne gawarwaki ba tare da sanin ahalin su ba.[11][12]

Kakakin rundunar Sojin Najeriya a lokacin, Kanar Sani Usman ya yi ikirarin cewa, a ranar 12 ga watan Disamba, ‘yan kungiyar ta Harkar Musulunci a Najeriya sun yi yunkurin kashe Janar Tukur Burutai a lokacin da yake tuka mota ta hanyar Zariya, ta hanyar toshe wani titi kusa da hedkwatarsu tare da jifa da duwatsu.

Yadda al'amarin ya shafi duniya

Anyi zanga zangar lumana domin yin tir da lamarin a sassan wasu birane na kasar Indiya, wadanda suka hada da Mumbai, Chennai, da Hyderabad.[13][14][15] Haka nan ma anyi a Tehran da Mashhad na Iran.[16]

Bincike

A cikin Janairu na shekarar 2016, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken musabbabin faruwar lamarin bisa ga jagorancin Maishari'a Mohammed Garba.[17][18]

Gano gaskiya

Ranar 1 ga Ogas shekarar 2016, kwamitin ya samu bayanin cewar sojoji sun harbe mutum 328 yan Shi'a.[19].

Sake Karanta

Manazarta