Paschaline Alex Okoli

Paschaline Alex Okoli wata 'yar fim ce a Nijeriya wacce aka fi sani da rawar Cordelia a cikin sitcom mai taken Jenifa's Diary . mafi yawancin lokaci an fi sanin ta a fim din Jenifa's Diary.

Paschaline Alex Okoli
Rayuwa
Cikakken sunaPaschaline Alex Okoli
HaihuwaNajeriya
ƙasaNajeriya
Harshen uwaHarshen Ibo
Ƴan uwa
Abokiyar zamasingle person (en) Fassara
Karatu
MakarantaJami'ar jihar Imo
Matakin karatuBachelor of Arts (en) Fassara
HarsunaTuranci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'aJarumi
Kyaututtuka
Imani
AddiniKiristanci

Farkon rayuwa da ilimi

Paschaline ta fito ne daga karamar hukumar Orumba ta kudu wanda ke cikin jihar Anambra, yankin kudu maso gabashin Najeriya . Ta yi karatu a Jami'ar jihar Imo inda ta samu digiri a Faransanci.

Aikin ta

Ta fara harkar wasan kwaikwayo ne a shekarar 2010 tare da fim din mai taken Definition Of Love. Amma duk da haka ta samu ci gaba a sitcom mai taken Jenifa's Diary inda ta taka rawar Cordelia, tare da yar wasan nollywood Funke Akindele .

Kyauta da gabatarwa

An zabi Paschaline ne don lambar yabo ta fim din City People don Kyakkyawar Sabuwar Jarumar Shekara (Ingilishi).

Rigima

Paschaline, wacce za a iya bayyana ta a matsayin 'yar fim mai rikitarwa ta jawo hankali sosai daga kafofin yada labaran Najeriya lokacin da ta bayyana cewa za ta iya yin tsiraici idan rawar da aka gabatar mata ta buƙaci ta aikata hakan sannan kuma; idan biya ya isa haka.[1][2][3][4] Kodayake a ma'aunin duniya wannan yawanci ba batun bane amma a cikin al'ummar Najeriya yawanci ana kyamatar abin.

Paschaline, koyaushe tana loda hotunan raunuka na kanta a Intanet[5][6] kuma yayin da wasu mutane za su yaba da wannan aikin kuma su yaba mata saboda wannan, akwai masu sukar kuma waɗanda ke tambayarta game da abin da aka ambata a sama.

Manazarta

Hanyoyin haɗin waje