Pape Latyr N'Diaye

Pape Latyr N'Diaye (an haife shi ranar 30 ga watan Nuwamban 1977) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Senegal wanda ya taka leda a matsayin mai tsaron gida.[1]

Pape Latyr N'Diaye
Rayuwa
HaihuwaOuakam (en) Fassara, 30 Nuwamba, 1977 (46 shekaru)
ƙasaSenegal
Karatu
HarsunaFaransanci
Sana'a
Sana'aɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
ƘungiyoyiShekaruWasanni da ya/ta bugaƘwallaye
AS Douanes (en) Fassara2002-2006
US Ouakam (en) Fassara2006-
 
Muƙami ko ƙwarewaMai tsaran raga

Sana'a

An haife shi a Ouakam, N'Diaye ya fara buga wasan ƙwallon ƙafa tare da ƙungiyar Entente Sotrac a cikin shekara ta 1993.[2] Ya koma AS Douanes a shekara ta 2002, inda zai lashe gasar cin kofin FA na Senegal sau uku a jere.[2]

N'Diaye ya ƙulla yarjejeniya da US Ouakam a 2006 kuma ya zama kaftin ɗin ƙungiyar da ta lashe Kofin FA na Senegal a 2006,[3] da kuma gasar Premier ta Senegal ta 2011 - gasar farko ta ƙungiyar a tarihinta na shekaru 60.[4]

N'Diaye bai buga wa tawagar ƙasar Senegal ba, amma an kira shi don wasan sada zumunci da Benin a ranar 7 ga watan Fabrairun 2007.[5] Ya kasance mai tsaron gida da ba a yi amfani da shi ba a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2012,[6] shi kaɗai ne ɗan wasan da ya taka leda a gasar cikin gida.[7]

Manazarta