Mpox a Najeriya

A cikin shekarar 2017, mpox ya sake ɓulla a cikin mutane a Najeriya bayan shekaru 39. [1] Ya zuwa karshen shekarar 2017, an samu a kalla mutane 115 da aka tabbatar sun kamu da cutar. [2]

Infotaula d'esdevenimentMpox a Najeriya

IriAnnoba de mpox (en) Fassara
Kwanan watan1971 –
ƘasaNajeriya
Yana haddasa2022 monkeypox outbreak (en) Fassara
2022 monkeypox outbreak in the United Kingdom (en) Fassara

Tarihi

Mpox a cikin 1971

Lokacin da aka gano cutar ta farko na ɗan adam a cikin DRC, Laberiya da Sierre Leone a cikin shekarar 1970, ba a sami bullar cutar ba a Najeriya, kuma binciken da aka yi na wasu namun daji da ba na ɗan adam ba a Najeriya ba a gano wata cutar mpox ba. [3] An fara gano kararraki biyu na mpox a Najeriya a cikin shekarar 1971. [4] Ɓullar cutar farko ita ce mace 'yar shekara huɗu, wacce ta fara a ranar 9 ga watan Afrilu. [5]

Ɓarkewar Cutar a shekarar 2017

A cikin shekarar 2017, mpox ta sake fitowa a cikin mutane a Najeriya bayan shekaru 39. [1] [6]

Farkon fitar da mpox daga Afirka ta hanyar mutanen da abin ya shafa ya faru ne a watan Satumba na shekarar 2018, lokacin da mutane uku da abin ya shafa suka yi tafiya zuwa Burtaniya da Isra'ila. [7]

A cikin shekarar 2021, an sami rahoton ɓullar mpox a Delta, Lagos, Bayelsa, Rivers, Edo, Babban Birnin Tarayya, Niger, da Ogun. [8]

Manazarta