Memunatu Sulemana

Memunatu Sulemana (an haife ta a ranar 4 ga watan Nuwamba shekara ta 1977) tsohuwar ƴar wasan ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Ghana wanda ta taka leda a matsayin Mai tsaron gida. Ta kasance memba na Kungiyar mata ta kasar Ghana .

Memunatu Sulemana
Rayuwa
Haihuwa4 Nuwamba, 1977 (46 shekaru)
ƙasaGhana
Karatu
HarsunaTuranci
Sana'a
Sana'aɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
ƘungiyoyiShekaruWasanni da ya/ta bugaƘwallaye
 
Muƙami ko ƙwarewaMai tsaran raga
Tsayi1.7 m

Ayyukan kulob din

A matakin kulob ɗin Sulemana ta buga wa Post Ladies a ƙasar Ghana. [1] Ta taɓa buga wa Pelican Stars wasa a Gasar Firimiya ta Mata ta Najeriya.[2]

Ayyukan ƙasa da ƙasa

Sulemana ta kasance ɗaya daga cikin yar tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Ghana a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta shekarar 1999, gasar cin kocin duniya ta mata na FIFA ta shekarar 2003 da kuma gasar cin kofen duniya ta mata a FIFA ta shekarar 2007.

Manazarta