Japhet N'Doram

Japhet N'Doram (an haife shi a ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 1966) ɗan asalin ƙasar Chadi ne kuma tsohon ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan gaba.

Japhet N'Doram
Rayuwa
HaihuwaNdjamena, 27 ga Faburairu, 1966 (58 shekaru)
ƙasaCadi
Faransa
Karatu
HarsunaLarabci
Faransanci
Sana'a
Sana'aɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football coach (en) Fassara
Hanya
ƘungiyoyiShekaruWasanni da ya/ta bugaƘwallaye
Tourbillon FC (en) Fassara1984-1988
Tonnerre Yaoundé (en) Fassara1989-199033
  Chad national football team (en) Fassara1989-19983613
  FC Nantes (en) Fassara1990-199719272
AS Monaco FC (en) Fassara1997-1998131
 
Muƙami ko ƙwarewaAtaka
Tsayi1.82 m

Shekaru 14 mafi girma a rayuwarsa ta kwallon ƙafa su ne na wanda ya shafe a tare da Nantes, wanda ya wakilta a matakai da dama. Ana yi masa alkunya da laƙabin Maye. [1]

Tarihin Rayuwa

N'Doram wanda aka haifa a N'Djamena, ya fara ƙwallo ne tare da klub ɗin Tourbillon FC na cikin gida, sannan ya shafe shekaru uku a Kamaru tare da Tonnerre Yaoundé, daya daga cikin manyan kulob a yankin Saharar Afirka . A shekarar 1990 lokacin yana ɗan shekaru 24, N'Doram ya sanya hannu a kungiyar FC Nantes a Faransa, inda ya ci kwallaye biyu a wasanni 19 a kakarsa ta farko a gasar Lig 1 ; samun damar sanya hanu a babban kwantiragin sa na farko ta zo ne a lokacin da Jorge Burruchaga na Ajantina ya tafi hutu saboda ya samu rauni inda a nan ne aka bashi lasisin sa hanu don maye gurbin abokin wasan nasa. [2]

Iyali

Ɗan N'Doram mai suna Kévin, shi ma ɗan ƙwallon ƙafa ne dake taka leda a Monaco. [3]

Ƙididdigar Wasanninsa

Bayyanuwa da kwallaye ta ƙungiyar, kakar wasa da kuma gasa
.KulabLokaciLeagueKofin [nb 1]Na duniya [nb 2]
AyyukaGoalsAyyukaGoalsAyyukaGoals
Tourbillon1984??????
1985??????
1986??????
1987??????
1988??????
Tonnerre1988??????
1989?15????
19903218????
Nantes1990-911923100
1991–922541000
1992–9331105000
1993–942684010
1994–9532121183
1995–9624152173
1996–9735210000
Jimla19272173166
Monaco1997–981311220

 

Manazarta

  • Japhet N'Doram at L'Équipe Football (in French)
  • Japhet N'Doram – French league stats at LFP – also available in French
  • Japhet N'Doram at National-Football-Teams.com