Bayelsa

Jiha ce a Najeriya

Jihar Bayelsa jiha ce dake kudu maso kudancin Najeriya, tana nan a tsakiyar yankin Niger Delta.[1][2] An kirkiri Jihar Bayelsa[3] ne a shekara ta alif dubu daya dari Tara da casa'in da shida (1996), kuma an cire ta ne daga Jihar Rivers.[4] Hakan yasa ta zamo daya daga cikin sabbin jihohin kasar. Ta hada iyaka da Jihar Rivers[5] daga gabas, da kuma Jihar Delta daga yamma, inda tekun Tekun Atalanta[6] ta mamaye yankin kudancin jihar.[2]

Bayelsa
Bayelsa State (en)


Wuri
Map
 5°N 6°E / 5°N 6°E / 5; 6
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birniYenagoa
Yawan mutane
Faɗi2,277,961 (2016)
• Yawan mutane107.91 mazaunan/km²
Harshen gwamnatiTuranci
Labarin ƙasa
Yawan fili21,110 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
MabiyiJihar rivers
Ƙirƙira1 Oktoba 1996
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwaExecutive Council of Bayelsa State (en) Fassara
Gangar majalisaBayelsa State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2NG-BY
Lambar Bayelsa
al'ummar Bayelsa
Cikin kasuwar Swali a birnin Bayelsa
Kogin bayelsa
Daya daga cikin cocin jahar bayelsa
Al adon balyalsa

Jihar Bayelsa da fadin fili na kimani na kilomita 10,773kmaq, wanda yasa ta zamo jiha mafi karancin fili a Najeriya.[7] Kuma tana da yawan jama’a kimanin mutum 2,394,725, (ƙiyasin shekara ta 2016), wanda ya sanya ta jiha mai mafi karancin mutane. Babban birnin jihar, itace Yenagoa. Douye Diri ne gwamnan jihar a shekara ta 2022, mataimakin shi kuma shine Lawrence Ewhrudjakpo.[8] Dattijan jihar sun hada da: Goodluck Jonathan, David Clark, Ben Murray Bruce, Emmanuel Paulker Izibefien da Evan Foster Ogola. A sanadiyyar kasancewarta a yankin Niger Delta, Jihar Bayelsa mamaye take da kogi da koramu, kuma kusan duka garin cikin ruwa yake, hakan ya jawo rashin cigaba ta hanyar gina hanyoyi.[9]

Ana amfani da harshen Ijaw a ko ina a jihar, tare da sauran harsuna kamar Isoko da Urhobo a tsaffin kyaukan jihar.

Bukukuwan bayelsa

Tana da kanan hukumomi 8: Ekeremor, Kolokuma/Opokuma, Yenagoa, Nembe, Ogbia, Sagbama, hi Brass da kuma Ijaw kudu. Bayelsa ta kasance gida ga Mutanen Urhobo a karamar hukumar Sagbama.[10]

A dalilin kasancewarta a yanki mai arkin man-fetur wato Niger Delta, tattalin arzikin Jihar Bayelsa sun ta'allaka ne akan aka man-fetur da ma'aikatun tace su. Yankin Oloibiri Oilfield inda aka fara hako man fetur a Najeriya.[11] Sannan zuwa shekara ta 2015, an kiyasta cewa tana samar da kusan kashi 30-40% na man fetur din Najeriya.[12] Ana yiwa jihar lakabi da “Glory of all Lands” sannan ita ke da tafkin gas mafi girma a Najeriya (18 trillion cubic feet).[13] Duk da cewa jihar ta mallaki manyan rijiyoyin mai kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin kasa, talauci yayi wa jihar katutu, hadi da gurbacewar muhalli[14] daga fesowar man fetur.[15][16]

Siyasa.

Ya zuwa shekara ta 2022, zuwa shekara ta 2022, Douye Diri ne gwamnan jihar, a yayinda Lawrence Ewhrudjakpo ke matsayin mataimakinshi.[17]

Kananan Hukumomi.

Jihar Bayelsa nada Kananan hukumomi guda takwas, Sune:

  1. Brass
  2. Ekeremor
  3. Kolokuma/Opokuma
  4. Nembe
  5. Ogbia
  6. Sagbama
  7. Southern Ijaw
  8. Yenagoa

Wuri.

Bayelsa na daga cikin jihohin kudancin Najeriya, jihar na nan a tsakiyar yanki Niger Delta. An cire Jihar Bayelsa daga Jihar Rivers, kuma tana daga cikin sabbin jihohin Najeriya.[18]

Jihar Bayelsa ta hada iyaka da Jihar Rivers daga gabas, Jihar Delta (jiha) daga yamma, a yayin da ruwan Tekun Atalanta ya mamaye yankin kudancin Jihar.[19]

Tarihi.

A karni na 20th, bukata na samar da sabuwar jiha da harshen Ijaw ke da rinjaye a yankin Niger Delta ya zamo sanannen abu. A tsakanin shekara ta 1941, zuwa ta 1956, an kafa kungiyoyi da dama dake goyon bayan samar da jiha na Mutanen Ijaw a yankin Kudancin Najeriya. Isaac Adaka Boro, wani shahararren dan gwagwarmayar Ijaw a shekara ta 1960, wanda aka haifa a Oloibiri yayi yinkurin ikirarin "Jimhoriyar Mutanen Niger Delta ("Niger Delta Peoples Republic") a shekara ta 1966.[20][21][22] Shugaban kasa na mulkin mallaka ya Sani Abacha ne ya kirkiri Jihar Bayelsa daga Jihar Rivers a ranar 1, ga watan Oktoban, shekara ta 1966.[23] An samo asalin sunan ne daga haruffan farko na sunayen kananan hukumomin ta: Brass LGA (BALGA), Yenagoa LGA (YELGA) da kuma Sagbama LGA (SALGA).[19]

A ranar 20, ga watan Disamban shekara ta 1999, ne sojojin Najeriya suka kaddamar da abinda aka fi sani da Kisan Kiyashin Odi. Ana kokanta akan ainihin yawan mutanen da aka kashe, duk da cewa, Nnimmo Bassey, Babban Darekta na Hakkin Harkokin Muhalli, ya sanar cewa farar hula mutum 2500, ne suka rasa rayukansu.[24][25]

Dangane da zaizayar kasa a jihar a dalilin ma'aikatun man fetur, anyi zanga-zanga da dama kamar "Rise for Bayelsa" da akayi don inganta samar da ruwan sha a kananan yankuna. A cikin shekara ta 2019, ne, gwamnatin jihar Bayelsa ta fara neman gwagwarmayar samar da mafita dangane da matsalolin gurbacewar muhalli a jihar.[26][27]

Tattalin arziki.

Jihar na daya daga cikin jiha mafi albarkatun man fetur a Najeriya.[28][29] A dalilin haka, akwai yawaitar man fetur a jihar. Duk da cewa jihar tana da arziki mai, jihar na samun karancin kudi daga kasafin man fetur a dalilin rashin daidaituwa a tsarin kasafi daga gwamnatin kasar.[30]

Yanayin kasa.

Bayelsa na zagaye da ruwan kogi da kuma koramu. Yankunan jihar da dama suna kewaye ne da ruwa wanda haka yasa ba iya riskar su ta tituna. Akwai gandun daji na "Edumanom Forest Reserve" a jihar. Tun watan Yunin shekara ta 2008, inda aka ga birin chimpanzee na karshe itace Niger Delta.[31] Sauran muhimman birane bayan Yenagoa sun hada da; Akassa, Lobia, Amassoma (the home of the Niger Delta University), Eniwari, Ekeremor, Aliebiri, Peretoru, Twon-Brass, Egwema-Brass, Kaiama, Nembe, Odi, Ogbia, Okpoama, Brass, Oporoma, Korokorosei, Otuan, Koroama, Okolobiri, Obunagha, Ogboloma, Sagbama, Olugbobiri, Peremabiri, Ekowe, da kuma Swali.

Akwai kuma ginin Akassa Lighthouse wanda ke nan tun shekara ta 1910.[32]

Harsuna.

Asalin harshen da ake amfani dashi shin harshen Ijaw, tare da yaruka kaman Kolukuma, Mein, Bomu, Nembe, Epie-Atisa, da kuma Ogbia. Kamar dai a sauran jihohin Najeriya, Turanci ne harshen gwamnatin jihar.

Jerin harsunan Jihar Bayelsa dangane da kananan hukumomin LGA da ake amfani dasu:[33]

Ekeremor, Bayelsa State
LGALanguages
BrassAbureni; Southeast Ijo; Ogbia; Kugbo
EkeremorIzon
Kolokuma OpokumaIzon
NembeAbureni; Southeast Ijo. Izon (Ijaw)
OgbiaAbureni; Southeast Ijo; Odual; Ogbia; Oruma
SagbamaBiseni; Isoko; Izon; Ogbah; Okodia; Urhobo
Ijaw ta KuduSoutheast Ijo; Izon
YenagoaEngenni; Epie; Izon; Ekpeye

Matsaloli na muhalli.

Gurbacewar iska

Wannan wani bakin hayaki ne da ke tashi a dalilin kona man fetur ba tare da ka'ida ba (ana kiransu a gargajiyance "wutan Kpo).[34] Wadannan mugayen sinadirai kan jawo rashin lafiya kamar Ciwon huhu na daji, matsalolin fata, matsala ta mashakar iska da dai sauransu. Ana iya ganin sauran illolinta kamar gurbacewar iska, ruwa da kasa wanda hakan sun jawo mutuwan tsirrrai, mutane da kuma dabbobi.[35]

Ambaliya.

Wannan sanannen matsala ne a Jihar Bayelsa saboda tana kan gabar Tekun Atalanta. Hauhawar igiyar ruwan teku ne muhimmin dalili na ambaliyar. Ambaliyar ta haifar da matsaloli ga al'ummomi da dama, dukiyoyi da kuma mutane. Kusan ko ina a Bayelsa na fuskantar matsalolin ambaliya, amma ambaliyar tafi tasiri a yankuna kamar Ekeremor, Ijaw ta kudu, Sagbama, Kolokuma/Opokuma da kuma Yenagoa wanda suke fuskantar barazanar duk shekara.[36] Rashin bin tsarin gine-gine na daga cikin dalilan dake assasa ambaliya a Jihar Bayelsa.[37]

Zubewar mai.

Wannan wani muhimmin al'amari ne dake kawo matsalar muhalli a Jihar Bayelsa a dalilin ayyukan kamfanonin man fetur a jihar. Zubewar mai na jwo illa ga gonaki, halittun ruwa da kuma mutane.[38] Kusan duk rana ana sanarwa Udengs Eradiri labarin zubar mai a Jihar Bayelsa, Niger Delta.

Kamar yadda yake fadi, a da zaki iya yin noma ka samu girbi mai kyau, ko kuma kaje kamun kifi ka kamo da yawa, amma yanzu zaka iya kwashe tsawon yini baka kama kifi ko guda ba.[39]

Wata matsala ta muhalli itace gurbacewar iska (Soot), wanda mafi akasarin mutanen Bayelsa na kukan cewa basu iya numfashi da kyau.[40]

Amma a shekara ta 2018, masu hanu da shuni sunyi kamfe mai taken "Save Rivers from this soot of death" wato a kiyaye koguna daga mutuwar Soot, a yankunan dake kewaye da ruwa.[41]

Ilimi.

Jihar Bayelsa nada makartu mataki daban daban wanda ke bayar da ilimi ga daukacin al'ummar jihar

Jami'o'i

Makarantun gaba da sakandare a bayelsa sun hada da

  • Jami'ar Neja Delta
  • College of Health Science Bayelsa.
  • Isaac Jasper Boro College of Education.
  • College of Nursing Bayelsa.
  • Bayelsa Medical University.
  • Bayelsa State College of Art and Science.
  • University of Africa.
  • International Institute of Tourism and Hospitality[42]

Sanannun Mutane.

  • Diepreye Alamieyeseigha, Tsohon dan siyasa a Najeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Bayelsa.
  • Diezani Alison-Madueke,Ministan Ma'adanai, Sufuri da Albarkatun Man-fetur[43]
  • MC Aproko, stand-up comedian.
  • Owoye Andrew Azazi, Chief of Army Staff na (Nigeria), Chief of Defense Staff a lokacin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo sannan kuma Mai ba wa shugaban kasa shawara akan harkar tsaron na shugaban kasa Goodluck Jonathan.
  • Noah Sarenren Bazee a professional footballer who plays for Bundesliga side Hannover 96.[44]
  • Isaac Adaka Boro, Jarumi a yakin basasar Najeriya (Nigerian Army)[45]
  • Timi Dakolo, mawaki[46]
  • Edmund Daukoru, Ministan Najeriya na Jiha akan Makamashi kuma ya kasance Secretary General na Kungiyar Kasashe masu Fitar da Man Fetur a shekara ta 2006, HRM[47]
  • Henry Seriake Dickson, tsohon gwamna kuma dan siyasa
  • Alfred Diete-Spiff, tsohon gwamnan Jihar Rivers, HRM[48]
  • Honourable Douye Diri dan kasuwa, dan siyasa kuma mai zartarwa wanda ke wakiltar mazabar Yenagoa/Kolokuna/Opokuma na 'yan majalisu.[49]
  • Tamara Eteimo wacce akafi sani da suna Tamara daga Angiama, karamar hukumar Ijaw ta kudu na Jihar Bayelsa. Mawakiyar R&B a Najeriya, marubuciyar waka kuma jaruma.[50]
  • Dan Etete Ministan Man Fetur[51]
  • Finidi George, Dan wasan kwallon kafa na Super Easgles[52]
  • Daniel Igali, Canadian wanda ya lashe kyautar zinare a gasar Olympic gold kuma jarumin duniya na dambe[53]
  • Ernest Ikoli, dan jarida kuma dan fafutukar neman 'yanci a lokacin mulkin mallaka.[54]
  • Goodluck Jonathan, Tsohon shugaban kasan Najeriya[55]
  • Heineken Lokpobiri, Ministan Jiha akan harkokin Noma[56]
  • Senator Ben Murray-Bruce mai wakiltar mazabar Bayelsa East Senatorial District a Majalisar Dokoki ta Kasa. daga Akassa na Jihar Bayelsa, Nigeria.[57]
  • Ebikibina Ogborodi, rijistran NECO na rikon kwarya[58]
  • Gabriel Okara, marubucin littafai kuma mahikayanci[59]
  • Melford Okilo, gwamanan Jihar Rivers[60]
  • Kemebradikumo Pondei, managing director na rikon kwarya a Niger Delta Development Commission
  • Ebinabo Potts-Johnson haifaffiyar Jihar Bayelsa, 'yar talla kuma 'yar wasan kwaikwayo.[61]
  • Samson Siasia, dan wasan kwallon kafa na Eagles kuma Coach[62]
  • Timipre Sylva, tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Ministan Najeriya mai ci na Jiha akan harkokin man fetur.[63]
  • Timaya, mawaki[64]
  • Patience Torlowei, mai tsara kwalliya kuma mawakiya


Manazarta.



Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara