Amarachi Okafor

Amarachi Okafor (an haife ta a shekara ta alif dari tara da saba'in da bakwai 1977) yar zane-zanen ce a Najeriya, kuma wacce take ayyukan ta akan al'adu, addini, tarihi, alakar jinsi, jima'i na dan adam, da kuma batutuwan da suka shafi duniya, kamar yaduwar cutar Ebola a Afirka. [1]

Amarachi Okafor
Rayuwa
HaihuwaUmuahia, 1977 (46/47 shekaru)
ƙasaNajeriya
Harshen uwaHarshen Ibo
Karatu
MakarantaJami'ar Najeriya, Nsukka
HarsunaTuranci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'aMasu kirkira


Rayuwar farko da ilimi

Okafor haifaffiyar garin Umuahia ce,[2] A shekara ta dubu biyu da biyu 2002 ta halarci kwasa-kwasan koyar da fasaha a Jami'ar Nijeriya kuma a shekarar dubu biyu da bakwai 2007, a wannan Jami’ar, ta yi digirin ta na biyu a bangaren sassaka abubuwa da kuma aikin koyo. [3]

Aikin ta

Okafor memba ce a El Anatsui ta Atelier a cikin shekarar 1990s.[4]

Okafor tana aikin zane-zane da sassaka. Ita ce mai kula da NGA (National Gallery of Art) a Abuja, tsakanin shekarar 2008 da kuma 2014.[5] A cikin 2007 ta ci nasarar zama a cikin unesco-Aschberg ƙungiya na masu zane-zane, da kuma Commonwealth Foundation Commonwealth Connections a cikin 2010. A shekarar 2014, ta kasance a lis din karshe a gasar kere kere ta kasa ta 2014, [6] kuma ta lashe kyautar Juror a waccan shekarar.[7][8]

Ta baje kolin ta a 2015 Jogja Biennal[9]

Manazarta

Hanyoyin hadin waje

  • Official website