Akeem Adeniyi Adeyemi

Akeem Adeniyi Adeyemi (an haife shi a shekara ta 1977) wanda kuma aka fi sani da Skimeh, ɗan siyasan Najeriya ne. Shi dan Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya ne mai wakiltar mazabar tarayya ta Afijio, Oyo West, Oyo East, Atiba West.[1][2][3] Dan sarkin garin Oyo ne Oba Lamidi Olayiwola III.[4]

Akeem Adeniyi Adeyemi
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

Rayuwa
Haihuwa1977 (46/47 shekaru)
ƙasaNajeriya
Karatu
HarsunaTuranci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'aɗan siyasa
Akeem Adeniyi Adeyemi in Oyo

Rayuwar farko

Iliminsa na farko ya zo a St Francis nursery da primary Oyo, St Andrew Demonstration Oyo, da kuma Olivet Baptist High School a Oyo. Ya yi karatun digiri na farko a jami'ar Benin.[1]

Sana'a

Ya shugabanci karamar hukumar Atiba daga shekara ta 2007 zuwa 2010. Ya yi aiki a matsayin shugaban riko na karamar hukumar Atiba a shekara ta 2011 zuwa 2014.[5] A zaben shekara ta 2015, ya tsaya takarar majalisar wakilai ta tarayya a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress kuma aka zabe shi a matsayin wakilin mazabar Afijio, Oyo east, Oyo west da Atiba federal constituency An sake zaben shi a shekara ta 2019.[2][6]

Manazarta